YAR MAKIYAYA CHAPTER 1

YAR MAKIYAYA CHAPTER 1
YAR MAKIYAYA CHAPTER 1 *Belel* K’auye ne kamar ko wanne cike da ahali iri daban daban d’auke da dabi’u iri iri, sedai duk da banbancin da suke da shi akwai abu d’aya da sukayi tarayya a kai wanda shi ne zaman lafiya, kamar dai ko wanne gari walau birnin ko k’auyen akan samu ahali mabanbanta wad’anda basu jituwa ko dai saboda matsayi ko kuma muk’ami. Mafi d’aukar hankali cikin k’auyen wasu ahali ne guda uku mabanbanta a matsayi da kuma yanayin tafiyar da rayuwa. Wannan labari ya fara ne daga zuciyar Wannan k’auyen wanda ya kasance shine mazaunin wani katafaren gidan sarauta mai cike da gargajiya da aladu, Masarautar da babu irin ta a wasu k’auyukan na k’etare. Daga wani b’angare na k’auyen akwai wani ahali wanda ya kasance shi na daban ne, jagora a wannan k’aramin ahali ya kasance *makiyayi* ne mai kiwon dabbobi kamar yadda kiwon ya zama gado ne gare shi haka ma ga iyalan shi sedai duk da ana musu kallon masu zama cikin lumana an gaza gane cewa cikin ko wanne ahali akwai nasu b’oyay…