YAR MAKIYAYA CHAPTER 15

YAR MAKIYAYA CHAPTER 15
YAR MAKIYAYA CHAPTER 15 Now that we are free from Ameer and company finally Suraj da Laila sun samu kwanciyar hankali. + Bacci take mai lafiya har k’ara luntsuma wa cikin bargo take hankali kwance , yana fito wa daga bathroom ya zauna gefen ta ya k’ura mata ido , ruwan da ke diga diga jikin shi ne yasa ta bud’e ido saida ta gama mutsitsika fuska ta zauna kawai suka had’a ido, wani shu’umin Murmushi ya sakar mata wanda babu shiri yasa ta koma ta kwanta gami da jan blanket ta rufe fuskar ta. Sosai ta bashi dariya ya d’an rik’e bargon zai bud’e ta Amma yaji ta rik’e gam gam ,dan haka ya sure ta daga ita har blanket d’in zuwa bathroom ya ajiye ta, kasa tsayuwa tayi ta zame ya rik’o ta yana dariya a hankali ya ce “Kiyi sauri Mun makara zamuyi sallah da k’adangaru”. Langab’ar da kai tayi ta marairaice kafin tayi magana ya rufe bakin ta da hannun sa yace “Na fahimta” saida ya jira tayi wanka sannan ya d’auko abin sa suka dawo d’aki ,bata b’ata lokaci ba ta zira Abaya ta sa hijab Sur…