YAR. MAKIYAYA CHAPTER 14 YAR MAKIYAYA CHAPTER 14 Abdul-malik , da nayi shiru ina zaton Wannan fad’an na tsakanin d’a da mahaifi zai wuce, tun yaron nan bai kai haka ba kuke wannan halin dalilin haka na saka shi dole ya biyo ka zuwa Belel living duk abokan sa da wasu muhimman abubuwa na rayuwar shi saboda a rayuwar shi kai kafi komai muhimmanci, amma Baku kwana biyu ba Suraj ya kirani saboda wannan halin naka, Nazo nan nima kasan ba don son zuwan nake ba amma sedai don inga na k’ara had’a kan ka da d’an ka amma maimakon abun ya ragu se yazo yafi na da far more than da. Yau ta kai ta kawo ga har zaka iya yi ma d’an ka illah da har zai kwantar da shi, jiya seda likita ya zo yau kam gashi chan ban san yadda zata kasance ba. Dan Allah Abdul-malik ka taimaka ka zauna da Suraj ko da Sau d’aya figure out your individual differences, your likes and dislikes sannan come up with a solution that will bind you together as one, but kafin nan ina so ka sani zan koma Egypt in kuka daidaita kan ku sannan ka cire wannan ak’idar…