YAR MAKIYAYA CHAPTER 13

YAR MAKIYAYA CHAPTER 13
YAR MAKIYAYA CHAPTER 13 Uncle Ahmad yayi abunda ya dace, tambayar anan shine shin Dad zai hak’ura ya kyale Suraj sannan ya amince da Laila a matsayin suruka? Ameer kuma fa? Wasan shi ya k’are ko kuma da saura? Saeed ma ba’a bar shi baya ba domin duk duniya babu macen da yake targeting irin Laila! + Anya kuwa tsugunno ta k’are??? 1:30pm Sanssayar iska ce ke shigowa ta window wanda yayi sanadiyyar fire wa da labulen d’akin yake yi ,hasken full moon ya hasko cikin d’akin daga windon hakan yasa d’akin ya bada wani launin haske mai ban sha’awa da burgewa. A tsanake ya bud’e idanuwan sa yana k’are ma d’akin kallo kafin ya yi yunk’urin tashi zaune ,rad’ad’in da yaji ne yasa yayi saurin rik’e cikin sa ya d’an saki k’ara gami da rufe ido. Da sauri ta d’ago kai tana murza idanuwa wanda daga ganin su kasan barci bai isheta ba daidai lokacin ya juyo yana kallon ta cike da mamaki. Zaune take a k’asa ta kwantar da kanta a gadon hannun ta cikin nashi. “Laila?” Ya k’ira sunan ta ,ta d’ago …