YAR MAKIYAYA CHAPTER 12 YAR MAKIYAYA CHAPTER 12 Kwalbar giya Brandy ita ce a hannun sa ,fuskar nan a dak’ile ga d’akin duk duhu ya mamaye se d’an hasken rana da ya hasko ta windon wanda bai kai ya haska d’akin ba , surutai yake ta yi shi kad’ai yana b’ab’atu + “Saeed Bro! Kai dai bazaka tab’a sauya halin ka na shan giya ba,” Cewar Ameer da ya shigo she toshe hanci yake. Wata gajiyayyan dariya Saeed yayi kafin da kyar ya ja jikin ya gyara zaman sa yace “Kamaaar yyadda bazzzakka t..taab’a daina gulma da shishigi ba ko? Tell me shin kkaaa samo yarinyar ko Yaya? Kasan yyadda nake son ta kuwa? I will spend the whole night with her! “ Shu’umin dariya Ameer yayi gami da shafa fuska yace “Na ga yarinyar ma, Amma bazan iya kawo maka ita ba because kawai zaka lalata mata rayuwa ne ka jefar da ita, bazan iya bari kayi haka ba, dan Allah baka da wani aikin ne se Shaye Shaye da neman mata ? Mutum kamar d’an bunsuru? Kwalbar giyan Saeed UA fasa har saida Ameer ya tsorata ya mik’e kafin yace “Look Ameer! Ni da kai kar ta san kar …