YAR MAKIYAYA CHAPTER 11 YAR MAKIYAYA CHAPTER 11 Tun had’uwar Suraj da Ameer basu sake had’uwa ba babu wanda ya shiga harkar wani se yau da suka tattara zasu koma Belel , Dad ya Matsa wai se an taho da Laila amma Ummi tayi y’an dabarun ta tace “ai zata koma Istanbul saboda karatun ta, Dad ya juya yace “ina Suraj d’in? ” + Daidai lokacin Suraj ya fito yana jan jakar sa ,sallama yayi wa su Ummi da Laila ya kuma tabbatar mata zai dawo kwana kusa ” Junaid ma suka yi sallama da Suraj Su Dad suna mota suna jira Suraj ya shigo suka ga ya nufi inda motar sa take ya jefa jakar sa ciki Wata shu’umin murmushi Ameer ya yi kafin ya ce “Aha ah? Daman ba tare zamu tafi da Suraj ba?” Se lokacin Dad ya lura da inda Suraj yake amma kafin ya ankare Suraj ya ja motar sa yayi gaba abunsa ,Murmushi Mom tayi yayinda driver ya ja mota suka wuce Airport direct, shi kuwa Suraj ya tafi by road abunsa hankali kwance ….. *three months later* Watanni uku ba wasa ba Laila ta yi clean da ita har wani d’an k’iba tayi ,duk inda Ummi zata tare suke…