YAR MAKIYAYA CHAPTER 10

YAR MAKIYAYA CHAPTER 10
YAR MAKIYAYA CHAPTER 10 Duk de yadda akayi akwai dalilin restlessness na Ummin Habeeb, a shafi na baya tayi magana a kan idanuwan Laila ko miye dalili? Bari mu garzaya muji yadda dinner zai fara….. “Sapna!” “Na’am Ummi!” Fitowa Sapna tayi daga d’aki tana kallon Ummi. “Ummi gani ” Murmushi Ummi tayi tace ” na tabbata Yayan ki Suraj ya baki labarin Laila ko ba haka ba?” “Eh Mom , meyasa kike tambaya? Ita da tak’i ta zo nan? ” Murmushi Mom tayi ta shafa kan Sapna tace “Idan kuma nace miki ta zo fa? Kuma tana tare da mu a cikin Wannan gidan? ” zaro ido Sapna tayi tace “Wait Mom! Na sanki you are not good at zolaya “ “Ba zolaya bane tana nan d’akin yanzu dare yayi amma gobe in Allah ya kaimu ina so ki kaita domin makeover, ina so ta chanja ki tabbata Suraj bai had’u da ita ba har se komai ya kammala it’s going to be a surprise ina fata kin gane?” Tsalle Sapna tayi ta mak’ale wuyan Ummi tace “wow! Ummi Yaya akayi kuka iya taho da ita? Nai miki alk’awari se Yaya Suraj ya kasa gane ta ma, Mom…