WATA FUSKA CHAPTER 1

WATA FUSKA CHAPTER 1
WATA FUSKA CHAPTER 1 Cikeda nutsuwarta take tafiya dukda yake yanayin ta kad’ai ya isa ya sanar dakai cewar lallai a gajiye take kuma kallon farko dazakawa fuskarta zaka tabbatar cewar lallai tana tattare da yunwa matsananciya…..batada sukuni batada cikakkiyar lapia tamkar wacce qwai ya fashewa aciki…. Iyakar inda aka direta bakin first gate na jami’ar usman d’anfodio d’in batada ko sisi!!! Batasan se yaushe zata isa gidansu ba dake low-cost…..Mataccen agogon dake wutsiyar hannunta daduk fatarshi ta gama tashi ta wurgawa kallo qarfe bakwai ta kusa….magrib kenan fa ta doso kai idan hakane tashiga ukunta da Baba iro…… Cira kafarta tayi taci gaba da tafiya sauri da sauri……se gab da isha ta isa k’ofar gidansu Babur d’in Baba iro ta wurgawa kallo ta tabbatar yau kashinta ya bushe batasan me aka gaya masa ba,batasan qazafin da za’a mata ba….batasan me ze mata ba!!!! Cikin dokawar qirji ta shura qafarta zuwa cikin gidan had’e da wara Bakinta dasunan yin sallam amma jin muryar Baba Azumi…