YAR TALLAH COMPLETE

YAR TALLAH COMPLETE
*YAR. COMPLETE * Littafin ya fara ne kamar haka  Tafe tAke tana rusa kuka wiwi,,,,,wiwi Duk ta hada miyau  majina da hawaye ta dame fuska gaba daya  Rungume take da tiren tallan tata wanda ba komai a cikinsa, sai ihu take kwararawa tana kiran wayyo kudina wayyo ni kudina Mutane sai kallonta sukeyi masu tausayi daga cikinsu su kirata suji abinda ya faru su lallasheta ta tafi  A haka taita saqawa ta lunguna harta iso layin gidansu  Tunda ta iso layin rabi,u wanda bai wuce dan kimanin shekara goma sha huduba kejiyo sautin kukanta yana duqe yana faman wanke wanke  Yai niyyar miqewa karaf sukai ido hudu da inna laure  Ta watsa masa wani irin kallo simi simi ya koma yaci gaba da wanke wanken  Tace munafuki dan iska wlh ka sake ka  tashi baka gama wanke wankennaN ba saina karya maka qafafu Ta qara jan tsaki ta hankade labule ta shige Daki Rabi,u yai saurin tsame hannunsa daga wanke wanken ya kwasa yai waje da gudu  A bakin kofar zauren sukai kicibus yace waya tabakine saude? Ta qara fashewa da wani kukan …