WANENE SHI CHAPTER 4

WANENE SHI CHAPTER 4
WANENE SHI CHAPTER 14 “Kayi shiru, I want to watch it quietly.” Nanne ta fad’a a hankali idnunta na kallon can gabansu, inda rana ke shirin fad’uwa, Tana kwance a jikinsa daga k’asan wata dogowar bishiyar kwakwa a bakin tekun dake ta ambaliya wani har yana tab’o kafafunsa dake mik’e. A can gabansu rana ce ke shirin fad’uwa, wani abu ne da bata tab’a gajiya da gani tun zuwansu wajen, wani abu dake k’ara mata jin kamar ba’a cikin duniya take ba sannan wani dake k’ara k’arfin imani a zuciyarta…ranar tayi wani irin ja sannan brightness d’inta yayi reflecting a kowacce kusurwa ta yadda ya bada hasken rainbow, tana kuma yin k’asa a hankali kamar tana lumewa cikin makeken tekun dake gabansu. Rayuwa ce ta kwanciyar hankali da nutsuwa, ba ruwan kowa dasu don wajen ba mutane sosai…saboda haka yadda zasu farantawa junansu rai shine kad’ai a gabansu. Sun ziyarci wajaje da yawa har da wasu island d’in dake kusa da nasu cikin irin speedboat da suka xo, a yanzu Nanne ta riga ta kware a shiga jirgin do…