WANENE SHI CHAPTER 13

WANENE SHI CHAPTER 13
WANENE SHI CHAPTER 13 Nanne ta k’ifta idanunta a hankali tana kallonsa, idanunsa na kallonta, kyakkyawar fuskarsa kusa da tata sosai! kamata yayi ta fizge daga rik’onsa, ta tashi ta bar d’akin, ta bar gidan, ta bar unguwar ma gabad’aya, ta tafi duk wani waje da zai nesanta ta dashi. Amma ta kasa ko motsi, idanunta na kallon nasa wanda ke cike da matsanancin rok’o irin na yaro k’arami sanda ya maka laifi, bayan hakan kuma akwai hanqoro na jiran abinda zata fad’a, a hankali ta shak’i sassanyan k’amshin dake fitowa daga jikinsa, wani k’amshi mai sanyi da dad’i, Taji zuciyarta na ayyana mata cewa k’amshin zai iya kwantar da hargitsin dake cikin kanta, saboda haka ta matsa a hankali ta cusa kanta cikin wuyansa sannan ta fad’i abinda yake gaskiyar zuciyarta. “Bana jin tsoronka…!” Da gaske ne ko kad’an babu d’igon tsoronsa da kalamansa suka sa mata, sai dai tarin mamaki fal da kuma rud’ani, gani take yi kamar a mafarki ko labari ne kad’ai abinda yake gaya mata zai faru, ta ture tunanin dake shi…