WANENE SHI CHAPTER 12 WANENE SHI CHAPTER 12 “….Amma banyi tunanin cewa raba jikinta da ruhin zai iya tab’a matsalarta ba yarima, saboda ni shaida ne akan wahalar da nasha kafin na iya juya zuciyar mahaifinta zuwa son yi mata aure yanzu, naga irin tarin k’aunar da iyayenta da ‘yan uwanta ke mata, ba zanso ace cikin sati d’aya kawai mun yi mata lahani ba. Sai dai tunda har an cire….” “Ba abinda aka cire.” Muryar Imran ta katse shi cikin kaushi. Ya juyo ya kalle shi har yanzu yana zaune so stiff ha tare alamar motsi ba, fuskarsa fayau take babu wani yanayin da zaka iya tsinta a ciki. “Kamar yaya? Na tabbatar… “Na sani…” Imran d’in ya sake katse shi. “…hasken yaje har gidan, amma ba abinda ya faru.” jaamil ya cigaba kallonsa mamaki na nunawa akan fuskarsa ko kuma rashin yarda ne? “Amma ta yaya toh…” “Nima ban sani ba.” Dukkaninsu suka yi shiru na wani lokaci kafin jaamil ya sake juyowa ya tambaye shi. “Toh me kake yi anan?” “Bugun zuciyarta ne baya bugawa daidai, I wanted to be sure saboda in nemo me ya same ta…