WANENE SHI CHAPTER 11 WANENE SHI CHAPTER 11 Da sauri ya taka steps d’in ya shiga ciki, sai da yazo dab! da ita sannan ya tsaya. “Sa’adha me ya faru? me ya same ki? wani yazo ne?” Yayi tambayar duk a lokaci d’aya sanda hannunsa ya lalubo nata, jikinta ya d’anyi b’ari amma nan da nan ya saki sanda ya shiga murza babban yatsansa a bayan hannunta. Cikin sheshshek’ar kukan ta girgiza kai. “Ba wanda yazo, na tashi ba kowa a gidan sai ni kad’ai, kuma nayi ta jin tafiya kamar za’a shigo amma ba kowa, sannan….” “Shshhh…” yasa d’aya hannunsa yana goge mata hawayen a hankali. Zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya tuna cewa ba taba zama a gida ita kad’ai ba, ta tashi a gida mai mutane da yawa ne dole yanzu taji bata saba ba. “I’m sorry habibty…kina ta baccinki mai dad’i sanda na fita shi yasa ban tashe ki ba, kiyi hak’uri dan Allah.” A lokacin wani gefen tunaninsa ya ayyana masa cewa shine Babban abin tsoron da ya kamata ta guda ma a yanzu. yasa hannunsa a bayanta yana zagaya shi a hankali sannan yana k’ara rada mata ta…