WANENE SHI CHAPTER 10 WANENE SHI CHAPTER 10 “Kin min shiru Sa’adha don Allah kiyi magana, ko har yanzu fushin ne?” Nanne ta sake tankwashe k’afarta akan gadon tana nannad’e bakin rigar filon dake kan cinyarta, a hankali tace. “Kana lafiya?” “Ina lafiya kuma yanzu da kika tambaya sai na k’ara jin lafiyar ta kama ni.” Tayi murmushi mai fad’i. “Ina jinki ki fad’a min sau nawa kika tuna ni bayan lokacin da kika ce min sai da safe?” Bata ce komai ba kamar yadda ya zata. “Ko sau d’aya ne kawai sanda kika yi min flashing?” Da sauri tace. “Ni ba flashing nayi ba ban sani bane kawai kiran ya shiga na zauna a kusa da wayar.” “Irin wannan bayani haka kamar laifi kika yi?…yanzu toh ba wannan ba, baki tambayeni sauran bayanin jiya ba.” Ta d’an hade girarta kad’an. “Wane bayanin?” “Bayanin koni WAYE mana, ko ba kya sonp kiji abinda nace wa baffa ya bani aurenki? ko kuma ki san wane irin miji zaki aura?” “Na san zaka fad’a min ai.” “Ta yaya kika sani? saboda kin san ina sonki?” Kamar baza ta amsa ba sai kuma tace. “Mhmmm.…