TSANANI CHAPTER 19

TSANANI CHAPTER 19
TSANANI CHAPTER 19 Cikin gida na shige tare da ajiye ledar da ya bani a gaban Adda, buɗewa tayi muka fara duba invitation card din don ganin ranakun da xa a gabatar da bikin namu, daurin aure ne a farko wanda ya kama za a yi ranar juma’a a babban masallacin juma’a na unguwar mu, sai dinner daga baya kuma sauran shirye-shirye suka biyo baya, yinin Innah ne a ƙarshe. Ware invitation din ta shiga yi, ta ware nata da na innah, tare da miko min na kawayena, miƙa mata nayi ta rage kasancewar ba ni da wasu kawaye na a zo a gani, sai dai ban sani ba ko Rukayya xata gayyato nata kawayen, naira dubu ɗari izuddeen ya bani, nayi abubuwan walimata gaba ɗaya na dam’kawa Adda kuɗaɗen. *********** A ɓangaren Innah Salamatu kuwa tuni ta gama rud’ewa, hankalinta gaba ɗaya baya jikinta ganin lokacin bikin Sa’adatu na ta matsowa ita babu labarin na ƴaƴanta, wajen salele ta koma yau a soron gidansa ta tarar da shi ya shimfida tabarma yana fito da hotunan yan matan da suka bashi ya samo musu mijin aure. Sal…