TATTALINTA CHAPTER 7

TATTALINTA CHAPTER 7
TATTALINTA CHAPTER 7 *B*alqees kuwa da kyar ta samu ta iya kaiwa safiya sabida kukan da tashi. k’arfe 5 da rabi ta mik’e da kyar tayi alwala tayi sallah tana addu’ar neman sassauci a gurin ubangiji sannan ne ta fara samun sauk’in zuciyarta sama-sama. Wajan k’arfe 7 Aamanee ta matsa kusa da ita har lokacin tana zaune kan sallaya tayi shiru idanuwanta a lumshe Aamanee ta janyo hannunta still bata bud’e idon ba Aamanee tace. “Wai har yanzu baki dena son guy d’in nan bane duk da yayi aure?!” Numfashi Balqees ta sauke tare da zare hannunta daga rik’o da tayi mata. bud’e ido tayi ta watsa su akan na Aamanee cikin razana tace, “Kuka kika yi Balqees?why?!” Bata bata amsa ba sai tambaya data wurga mata. “Yayya Aamanee yaushe zaku koma gida?!” “Bin mu zaki yi ne?” Ta kuma yi mata tambayar itama tana faman kallonta zuciyarta nayi mata sak’e-sak’e da yawa. Balqees ta share kwallar da ta zubo mata akan kuncinta sannan tace. “Eh..” Aamanee ta gyara zama tare da sake kamo hannun Balqees tace, “Go…