TATTALINTA CHAPTER 6

TATTALINTA CHAPTER 6
TATTALINTA CHAPTER 6 *S*ultan na yin parking Yusif yayi saurin bud’e k’ofar ya fito,k’ok’arin d’aukar Balqees yake yi cikin sauri da tafasar zuciya Sultan yayi saurin ture shi tare da zabga mai harara idanunshi jawur yace. “Karka sake ka ta6a ta Yusif, ka bari idan aka ce ta mutu sannan ne zaka iya zuwa ka d’auketa dan naga alamar rayuwarta kake nema.” Wuru-wuru da idanuwa Yusif yayi yana faman hura baki Sultan ya d’akko ta dai-dai lokacin nurses suka zo da gado ya d’ora ta akai,cike da mamaki sister Hadiza ta kallesu tace. “Ohh kaga wata jaraba,kullum a gida d’aya mutum biyu ne basu da lafiya.idan ya warke sai ta kama, idan aka samu ta warke shima sai ya kama kamar tsafi.” Wata nurse d’in ce dake gefenta ta kalli Hadiza bayan ta harareta suna sauri zasu kai Balqees cikin emargance tace, “Ke dai Hadiza kin fiye sa ido d’ai-dai kune baki sani ba a duk masu zuwa cikin asibitin nan.” Dai-dai lokacin suka shiga da Balqees cikin d’akin.a reception kuwa Sultan na ganin an shiga da…