TATTALINTA CHAPTER 4 TATTALINTA CHAPTER 4 *H*ajiya kaka dake cikin d’akinta ta fito da kyar domin girma yazo mata sosai,d’akin Balqees ta shiga hannunta rik’e da casbaha tana shiga taga sai faman kokawa akeyi tsakanin Yusif da Balqees ta k’arasa gurin tana caud’a masa cikin fad’a take cewa. “Wai kai wane irin wawan yaro ne ah?iskancin naka yakai ya kawo saika lalata ‘yar Amana ko?toh ubanka zakaci wawa kawai tashi ka barmin gida ko ranka ya b’aci.” Tashi yayi tsaye ya matsa kusa da kaka ai kuwa ta caula mai caibin ba tare da yaji zafi ba yace mata. “Ke daure a d’aura mana aure a cikin week d’innan idan ba haka ba kuma k’ad.” Yayi kwafa tare da lakucewa hajiya kakan hanci ya fita, k’arasawa tayi gurin Balqees tana kallonta cikin sanyin murya tace, “Kinga tashi kirawo min Muhammad gara ya maidake can gidan su gara can da nan maza kira min shi a wayarki.” Balqees na kuka ta d’auki wayan ta kira Sultan,tana jin ya d’aga ta bawa hajiya kaka tace maza-maza yazo tana son ganin shi,Sultan yace tabari ayi…