TATTALINTA CHAPTER 2 TATTALINTA CHAPTER 2 *B*ayan kwana biyu da dawowarta kwance take a cikin d’aki tayi ruf da ciki tana danna waya kamar daga sama taji an warce, saurin kallon gurin tayi karaf suka had’a idanuwa da brother Yusif yana kashe mata ido d’aya, shareshi tayi ta mik’e ta d’auki d’ankwalinta ta d’aura sannan ta fara gaidashi. “Brother Yusif ina yini?” “Kalau qis ya jin dad’i naga kallon pic’s kike yi ko update kikeyi ne?!” “No ni bana saka hotuna a istargram sai dai na kalli na wasu kawai.” “Meyasa bakya so?!” “Haka nan.” “A’a kodai kin tsaida miji ne shi yasa bakya d’orawa?!” Dariya tayi tana kallonshi ganin irin kallon da yake bin ta dashi ne yasa jikinta shiga cikin rud’ani tayi karfin halin cewa, “Eh kuma gashi yana da kishi idan ya gani sai munyi fad’a dashi.” Baki Yusif ya tab’e sannan ya samu guri ya zauna,ajiye wayan yayi a gefenshi yana kallonta cikin wani salo wanda shi kad’ai yasan manufarshi yace mata, “Yanzu idan nace zan aureki zaki yadda Balqis?” Daram kirjinta ya buga tayi saurin kallonshi …