TATTALINTA CHAPTER 11
TATTALINTA CHAPTER 11 *Ya* kyalkyale mata da dariya yana k’arasawa cikin kitchen d’in. Ba k’aramin haushin dariyar taji ba, toh ma wai me tayi da zai shigo ya dinga yi mata dariya, ta juya taci gaba da gyaran kyan miyarta tama fasa d’akko abubuwan. A bayanta ya tsaya bayan ya samu ya tsaida dariyar sa da kyar. Sak’alota yayi bayan ya sunkuya dai-dai tsawonta ya riko kugunta tare da kai mata pack a kumatunta yace. “Baby ya aka yi ne?!” Banza tayi mai ganin haka shi kuma yasa shi d’aukarta ta bayan ta ya fita da ita sai faman zillewa tak’e yi tana cewa ya sauke ta bata so amma yak’i har saida suka k’arasa kan kujerar parlor sannan ya direta yana dariya yace. “Baby me zaki yi a cikin kitchen ne..?” Cikin turo mai baki da yatsina fuska tace. “Ba girki zan yi mana ba, kuma duk an wani tashi an d’ora abubuwan a sama, kuna kazo kaga na kasa d’akkowa a memakwan ka d’akko min shine zaka tsaya yi min dariya.” Kissing d’in lab6anta yayi tare da matseta a jikinsa, rarraba idanuwa yayi tare da h…