TATTALINTA CHAPTER 1 TATTALIN TA CHAPTER 1 *A* hankali nake k’arasawa kusa dashi daga inda nake da tsaye a gefe ina kallon, matattakala shiga gurin nabi cikin wani irin taku wanda bana son ajine bare a gane d’aukar rahoto nazo yi na isa kusa da shi inda bazai hangoni ba sai dai ni na ganshi na tsaya. Kallon inda suke yake yi cikin wani salo kamar baya son a gane hakan, kallon shi nayi dan tantance kaman nin shi da tsarin shi. wankan tarwada ne dogo mai nagartaccen tsayi, ma’abocin ingarman jiki, da cikakkiyar fuska d’auke da yalwar dara-daran idanu da wadataccen dogo siririn karan hanci mai kyau, ga kuma yalwar girar idanu kwantac ce game da kwantacce mai laushi na gashi a kowan ne ga6a da take buqatar hakan. Kallon su ya sake yi ta gefen ido ya hango yayan na shi ya zauna a kusa da ita, ita kuma sai murmushi take yi tana rufe fuska wanda da alama kunyar shi take ji, bayan ya zauna ne yayan shi ya kalle ta shima yana murmushin a hankali yake jiyo maganar su ya kasa kunne ya jiyo me zasu ce yaji yayan nashi…