SAMU CHAPTER 4

SAMU CHAPTER 4
SAMU CHAPTER 4 Zuwairah Ihu ta tsala tana yarfa hannu, wayoo Allah na ta sake kafa ta wangale tana ganin jinin na tsiyaya.. 3 A daddafe ta kamo wayar ta sai ta rasa waye guda daya zata kira gashi bata shiri da ko mutum daya daga dangin jabir… Uwa uba mahaifiyar sa ummah.. Kuka ta fashe da shi, tana wayyo wayyo tuni ido ya raina fata tana nishi sama sama, Chan da abun ya tsanan ta ta shiga rolling a kasa tana damke ciki data ga haza ta yanke hukuncim kiran maman abdu da suka hadu da ita wajen siyan kayan mata Anguwan su na dan nisa amma haka ta daddafa ta zo, ITa taimaka ta kai zuwaira asibiti akan zata biya ta kudin ta tunda yau jabir zai dawo. Anan aka bata gado aka duba ta, Da shike ma asibitin ba wani mai karfi bane Ya sa aka musu komai yar sharp sharp.. Likitan ya sanar da zuwairah ciki ne ya zube acikin ta ،sannan tana bukatar proper medical check up.. Ita dai Bata damu na tunda tadan ji dama dama Basu ma gama shan ruwan ba ta sa maman abdu ta dawo da’ita gida ana neman karfe hudu na yam…