SAKAMAKO 5 SAKAMAKO 5 Haka rayuwan su ya kasance a gidan kwana biyar kenan yanzu captain ya dawo quiet bai cika magana ba sannan ba ya yarda taga damuwa da nadaman dake kan fuskan sa game da ita.. Duk iya rikici suhan takan masa amma sam baya amsa ta sumtimes in abun ya ishe sa sai ya soma romancing dinta ko don ta tsorata tayi shiru ta dena gaya masa magana….ya sani sarai suhan tana so taji daliliin abu biyu da suka faru a kwanakin ” na farko tasan yace zai hada ta da mum sannan ya sake ta..na biyu kuma meyasa ya tara da ita meya ke nufi da hakan? Duk wannan amsa ne wanda ya qudira aransa sai ta warke ta dawo normal zai zaunar da ita suyi don shikan sa a birkice yake yana neman maslaha da zuciyan sa game da abun da ya aikata tun farko.. Ranar da safe tana zaune ta kammala waya da ummahn ta kenan ta kumbura fuska tayi tagumi don haushi ke damun ta…”sam ta kasa fada ma su ummah yanzu bata zuwa aiki tsoron ta kar ummah ta tambayi dalili” allaura ya tono garma…gashi ta lura tun ranar kusan kullum ta …