YARIMA KHALEED CHAPTER 1 YARIMA KHALEED CHAPTER 1 ••••••••LUXURY HOTEL NEW DELHI,suite ne sanye jikinsa wanda suka matuƙar masa kyau, a hanƙali yake sakkowa cike da ƙasaita daga matattakalan benen Securities ne ke biye dashi baya da gabansa da gefensa, fitowarsu haraban hotel ɗin ya miƙa hannu tare da amsar baƙin glass ɗinsa ya saka. ɗaya daga cikin haɗaɗɗun fararan motocin dake pake ƙirar benz ya nufa, buɗa masa akai ya shiga, bayan tabbatar da zamansa ya daidaitu driver yaja motar yabi bayan biyun motocin dake gaba sannan ukun bayansa suka biyosa shima. hawansu titi jiniya ta karaɗe ko’ina,DLF mall New Delhi india suka tsaya, inda motoci ke aje sukai park,tsayuwar motarsa da sauri aka kewayo aka buɗa masa. sai daya ɗanja time sannan ya ziro da ƙafafunsa dake sanye cikin fararan takalma waje. tsaye yayi tare da lumshe ido inda ya shaƙi sanyayyar iskar data kaɗo zuwa hancinsa. doguwar ajiyar zuciya ya sauke, takawa yay yana tafiya a hankali zuwa inda wasu resting chairs suke. glass ɗinsa ya zare yana kallon wurin jiki…