WANENE SHI CHAPTER 9 WANENE SHI CHAPTER 9 Another day… without your smile. Another day… just passes by. But now i know, how much it means. For you to stay right here with me. The time we spent apart will make our love grow stronger. But it hurts so bad I can’t take it any longer… I wanna grow old with you….. 1 Wakar ta katse a daidai nan sakamakon kiran daya shigo cikin wayar. yadda ya tallafe bayan kansa da duka hannayensa biyu ya masa dadi, saboda haka bai ko motsa ba har kiran ya katse. Yana kwance ne akan irin dogwayen kujerun nan na bakin beach, yana jin iskar wajen mai sanyi da dad’i na kad’a kowanne particles na gashin jikinsa, ya mak’ala earpiece a kunne sannan idanunsa a bud’e yana kallon adon taurarin dake haskawa a samansa. Adonsu mai kyau, yadda suke shining akan black universe d’in samansa. ya had’e dogwayen gashin idanunsa waje d’aya sannan ya sake bud’e su, taurarin na da kyau, idonsa ya gane masa kuma kwakwalwarsa ta fad’a masa, amma hakan ya kasa tafiya cikin zuciyarsa. Zuciyarsa da ta kasa nutsuwa tu…