WANENE SHI CHAPTER 7 WANENE SHI CHAPTER 7 Nanne ta bud’e idanunta a hankali tana jin kamar ta tashi daga bacci. K’amshin turare da warin izal ne suka fara shiga hancinta kafin hayaniyar mutanen d’akin ta ziyarceta. Idanunta suka ci karo da silin fari, a jikinsa kuma akwai fanka wadda ke juyawa da k’arfi. + A ina take ne? Don tabass nan ba d’akinsu bane. Sai kuma kwakwalwarta ta tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta, tun daga tahowarsu titin Al-karsma gar zuwa sanda tazo tsallaka titin nan da sanda wata mota da bata san daga ina take ba tayi sama da ita. “Ta farka ne?” wata murya da bata san kota waye ba ta kutsa cikin kunnenta. “Ai kuwa kamar idonta a bud’e yake.” Wata ta matso jikin gadon sannan ta kira sunanta, a lokacin maganganun mutane daki suka fara raguwa, saboda haka ta yunk’ura sosai sannan ta ware idanunta, ai kuwa fuskar Aunty nafisa ta fara cin karo da ita, sai ta Rahma sannan kuma Inna. Tayi k’okarin mik’ewa amma gabadayansu suka dakatar da ita. A sannan ne inna ta fara kuka tana fad’i…