WANENE SHI CHAPTER 5 WANENE SHI CHAPTER 5 RANAR LARABA! + Wajen karfe Takwas saura kwata, Imaran yayi parking motarsa a cikin kanfaninsu, ya fito ya d’an kalli yawan motocin gurin sannan ya gyara tie d’insa ya nufi cikin building d’in “Barka da zuwa ranka ya dad’e.” malam iliya dake zaune a kusa da k’ofar elavator ya gaishe shi. “Barkan mu dai Baba, fatan ka tashi lafiya.” Ya amsa da murmushi, ya san yanayin kallonsa da yake masa na cewar yau ya makara ne, wanda shima bai san ya akayi hakan ta faru ba, da kyar ya iya tashi yau saboda nauyi da jikinsa ya masa da kuma wani irin jiri da ya dinga ji. Sai da yasha duk wasu magungunan kariyarsa harda wanda ya shanye gaba daya ma sannan ya iya shiryawa da kyar ya fito Ya shiga cikin elevator d’in ya danna floor na shida, ya d’an jingina kansa da gefe yana kallon yadda numbobin ke canjawa suna yin sama. Tunaninsa ya koma kan jaamil da ya dawo shekaranjiya, dole ne a yau ya neme shi su san yadda zasu shawo kan matsalar nan, tunda ba jikinsa ne ke ciwo ba balle yace irin …