WANENE SHI CHAPTER 4

WANENE SHI CHAPTER 4
WANENE SHI CHAPTER 4 Ta murda ta jijjiga, ba alamun kofar zata bude. Zuciyarta ta shiga dukan tara-tara don a cikin tunaninta ba zata iya tuna inda mukullan k’ofar nan suke ba, in ma suna nan din kenan. “Akwai mutum anan?” Ta daga muryarta da karfi ta kira. “Idan wani na jina dan Allah a bud’e kofar ta rufe dani.” Shiru ba motsi, sai tashin kid’an waje da take jiyowa kawai daga nesa. Hannayenta dake rike da k’ofar suka shiga rawa, ta cigaba da tsayawa a wajen tana rarraba zuciyarta waje-wajen neman mafita, aikuwa take ta tuna da tagar dake cikin d’aki wadda zata fitar da ita jikin barandar saman, ta koma da sauri wajen ta shiga kokarin zura mukullin, sai dai bata kai ga sawa ba lokacin da hasken tvn bayanta ya sake kamawa, sannan muryoyin cartoon d’in dake magana da larabci ya karad’e ko’ina a d’akin Ba shiri ta cusa mukullin ta murda sanna ta fad’a ciki, ta ture net d’in daya rufe tagar sannan ta dira waje, bata san cewa sauri take ba sai da ta kusa yin karo da wata mata dake kokarin shig…