WANENE SHI CHAPTER 3 WANENE SHI CHAPTER 3 Wai ya na gansu ne kala-kala?” + Amina ta tambaya tana warwara katunan dake kan bencinsu. Nanne ta tsotse kwallon agwalumar bakinta tace “Wai fa bayan events ukun da za’ayi kowacce sun had’a nasu daban zasu yi da yan’uwansu, shine baffa yace shi ‘yanuwansa kala d’aya ne kuma dole zasu je na kowa don haka suyi a rana daban-daban.” “Toh ai dates din sun hargitse min, kati wajen bakwai wanne za’a fara?” “Kinga fa, event din farko shine wankan amare ranar litinin, shi inna ce ta hada da daddare za’ayi, sai kamu washegari talata shima a gida za’ayi, laraba mother’s eve na kowa da kowa a wannan event center din, Alhamis shine bikinsu hajiya Babba suma ga inda zasu yi, juma’a na mama rabi itama da wajenta, Asabar kuma nasu mama halime, sai lahadi a d’aura aure kowacce ta kama gabanta.” “Tabdijam! Wannan ai gajiya zaku yi, bikin ba zai taba dadi ba.” “Ko dai su gaji, an gaya miki kowanne zanje, ni kawai bak’in cikina za’a hana ni baccin safe weekend.” “Toh ba kowanne zaki ba ni ki…