WANENE SHI CHAPTER 2

WANENE SHI CHAPTER 2
WANENE SHI CHAPTER 2 An kawo lefe kamar yadda kowa ya zata, akwati goma sha shida da kuma bayanin cewa bayan auren a can nijar jamilan zata zauna, anci an sha a gidan kamar gidan biki sannan kuma an tarbi mutanen nijar cikin girmamawa kafin su tattara su tafi wani guest inn dake bakin titin unguwarsu inda baffa ya kama musu d’akunan kwana. Su mama rabi an samu abinda ake so, wato lefen ‘yarta yafi na kowa, don na Aisha guda goma sha biyu ne, nasu maryam da nafisa kuma takwas-takwas. Saboda haka sai washe baki take yi anata hidima. Duk wannan abin ya faru ne bayan an gama tashin hankali da bala’i a gidansu hafsa, inda nanne ta rufe idonta ta zage ta tas! a gaban ‘yan gidansu, ba don rahma bama da abin ya kaisu harda kokawa don sun tarar maman su hafsar da kishiyarta basa nan sai ‘yan matan gidan kawai, amma duk da yawansu ba wanda nanne ta kyale a cikinsu, sai da rahma taga abin zai koma kokawa sannan ta jata da kyar suka bar gidan. Suna zaune bayan sallar isha a barandar dake kofar kici…