TSANANI CHAPTER 9 TSANANI CHAPTER 9 Sun ɗauki lokaci mai tsawo suna jiran dawowarsu Adda saratu amma shiru babu su babu dalilin su, sun yi jira ya kai na awa biyu har sai da suka fara gajiya, ganin ba su da niyyar dawowa ne yasa suka ɗauki hanyar xuwa wajen innar Sa’adatu don jin wajen da suka tafi da kuma inda aka boye Sa’adatu. + Zaune take a daki ta idar da sallar la’asar tana ta jero addu’o’i a kan Allah ya kawo musu mafita ita da Sa’adatu, bayan ta kammala ne ta janyo Kur’ani ta fara karantawa. Hayaniyar jama’a ta ji a tsakar gidan a yadda alama ta nuna dukkan matan gidan ne suka hallara a tsakar gidan suna jin abinda Baban Sa’adatu yake faɗa musu, gaba ɗaya sun bashi hankalinsu suna sauraren abinda yake faɗa, ganin ba a kirata ba kuma ba a sa da ita bane yasa tayi xamanta a daki ta cigaba da karatunta, daga can taji kamar har da Malam Jibo ake maganar don taji irin muryarsa duk da dai bai fi gani ɗaya ta taɓa yi masa a rayuwarta ba, amma kuma magana ɗaya biyu sai taji an kira sunan Sa’adatu, wannan…