TSANANI CHAPTER 5

TSANANI CHAPTER 5
TSANANI CHAPTER 5 Yau kusan satina ɗaya a gidan Adda saratu rayuwa nake mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali babu wani abu da ke damun xuciyata, sbd Adda saratu mace ce mai kirki babu wani abu mara daɗi da take min ta ɗauke ni tamkar yar da ta haifa a cikinta, sai dai abu ɗaya da ke damuna shi ne yawan tunanin innata da nake yi a halin yanzu, sbd ban san halin da take ciki ba, tunda Adda saratu da kanta taje gidan namu don shaida mata cewa ina wajenta, sai aka ce mata an koreta daga gidan, ga rashin masoyina da aminiyata wanda ban san halin da suka kasance ba bayan tafiyata, ban san lokacin da zan daina kewarsu ba Tsaye nake a kitchen ina mayar da kwanukan da na wanke, Adda saratu ce ta shigo “Sa’adatu anya kina so mu yi tafiyar nan kuwa, ki kalli agogo har ƙarfe ɗaya saura tayi” da sauri na duba agogon da ke nanne a kitchen din “ayya ban kula lokaci ya tafi haka ba bari nayi sauri na ƙarasa abinda nake tunda nayi wanka baxa mu bata lokaci ba” sauri nayi kammala abinda nake yi, ha…