TSANANI CHAPTER 4 TSANANI CHAPTER 4 Tun lokacin da innah salamatu ta je gidan su Izuddeen Mama bata ƙara samun kwanciyar hankali ba kullum a cikin tunanin yadda zata bullowa al’amarin take yi, ga shi ta kasa fadawa kowa kuma ta kasa tunkarar Izuddeen da maganar, ita kaɗai ta bar abin a ranta yana yi mata yawo, saboda har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya a kan gaskiya ta faɗa mata ko akasin haka Yau dai ta yanke shawarar faɗa masa ko zata ji sanyi a ranta, tashi tayi da kanta ta nufi dakinsa, sai dai tayi rashin Sa’a baya nan dakin nasa a kulle, dawowa cikin gida tayi sannan ta ɗauki waya ta kira shi cewa tana kiransa da gaggawa. Yayi nisa da gida amma haka ya daure ya juyo saboda yadda mama ta jaddada masa cewa tana son ganinsa da gaggawa. Gabansa ne ya riƙa faduwa Allah yasa dai alkhairi ne yasa ta kira shi don tunda suke bata taɓa yi masa irin wannan kiran ba. A daki ya sameta tayi tagumi tana tunani, har yayi sallama bata san ya shigo ba sai a karo na biyu da ya sake yi sannan ta san da shigowarsa, cik…