TSANANI CHAPTER 3

TSANANI CHAPTER 3
TSANANI CHAPTER 3 Hawaye na gani ya cika idonta da sauri na fara tambayarta “menene ya sa ki kuka Rukayya? Kiyi hakuri insha Allah alkhairi ne xai same ni, ki daina damuwa da halin da na shiga a yanzu wata rana sai labari” ƙarfin halin mikewa tayi tare da riƙe hannuna “tashi mu je wajen innah hankalina baxai kwanta ba har sai mun samu amsar abinda malam ya fada miki, to ni me ma yake nufi da Maganar nan ni fa na fara tsoron al’amarin sa,, saboda tunda yake tare da mu bai taɓa kiranki ya faɗa miki wani abu makamancin wannan ba, gaskiya idan wani abu ya faru Baba ya cuce mu” tashi nayi ba tare da nayi mata gardama ba muka riƙe hannun juna muka tafi gida Izuddeen muka hanga tun daga nesa yake mana murmushi babu wacce ta iya mayar masa da martanin murmushin da yake mana saboda dukkanmu muna cikin damuwa, ya lura da yanayin da muke ciki, sauri ya riƙa yi har yana tuntube don yazo ya tarar da mu. Sallama yayi mana gaba daya muka amsa Rukayya ce tayi ƙarfin halin yi masa magana “Izuddeen ya kak…