TSANANI CHAPTER 2
TSA NANI CHAPTER 2 A makaranta ma dai ban wani mayar da hankali nayi karatu ba saboda yawan tunane-tunanen da na riƙa yi har malam sai da ya fuskanci ina cikin damuwa. Tare da Rukayya muka dawo muna tafe muna hirar mu irin ta kawaye, gidanmu tace zata je saboda kawai tana so ta ɗebe min kewa na manta da dukkan damuwa ta, sannan kuma ummansu bata nan ko ta koma gidan babu abinda zata yi sai zaman kaɗaici + Sallama muka ji a bayanmu gaba ɗaya muka waiwaya ba tare da mun amsa sallamar ba, wani kyakkyawan saurayi ne mai cikakkiyar kamala sanye yake da shadda fara ƙall wacce aka yiwa aiki da brown din zare, takalminsa ma brown ne, kansa babu hula wanda Hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawan kwantaccen gashin sa, bai gajiya ba wajen sake yi mana sallama wucewa muka yi muka kyale shi ba tare da mun amsa masa ba, biyo bayan mu yayi. “Haba bayin Allah bai kamata ku ƙi amsa min sallama ba, ga alamu sun nuna min ku malamai ne baxa ku wulakanta ni ba wannan dalilin ne ma ya ja ni har nayi kwadayin y…