TSANANI CHAPTER 18 TSANANI CHAPTER 18 Zaune nake bisa kujera ina wanke kwanunkan da muka bata, yau ni kadai ce a gidan duk kaɗaici ya dame ni ya’yan Adda duk sun tafi islamiyya, sauri nake na ƙarasa abinda nake yi na tafi wajen Rukayya, mu yi hirar mu ta xumunci, farin ciki ne lullube da zuciyata sbd na san izuddeen ya kusa zama mallakina har abada, sallamar da Adda tayi ne ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi. + Tun kafin ta karaso take min murmushi “Amarya kin yi goshi, kinga abin arxikin da aka zubo miki kuwa? Abin dai sai wanda ya gani, kaya kamar ba da kuɗi yake siyan su ba, gaskiya yaron nan yana sonki da yawa” Ta faɗa tare da karaso wa kusa da ni gami da cire mayafin da ke jikinta gefena ta samu ta xauna. Cikin jin kunya nayi mata sannu da xuwa, ban nemi jin abubuwa da aka zuba min ba, sbd na san ina yin magana Adda xata ce ba ni da kunya, shi yasa na mayar da hankalina wajen aikina. Sake yi min magana tayi. “Baki ce komai ba Sa’adatu, ko alkunya kike min?” A hankali nace “To me xan ce Adda!?” Mu…