TSANANI CHAPTER 17 TSANANI CHAPTER 17 Kwance nake bisa gadona ina jujjuya wayata, ba komai nake jira ba sai shigowar text ko wayar izuddeen yau da tunaninsa na tashi, ƙara kallon wayar nayi tare da sakin murmushi ina tuna yanayin da nake samun kaina a duk lokacin da naji muryarsa. + A dai-dai lokacin ne Adda ta shigo dakina, ɗan dukan kafata tayi a hankali na waigo na kalleta tare da yin murmushi kaɗan. “Sannu da shigowa Adda” Ƙarasa mi’kewa nayi tare da xama kusa da ita. “Yauwa Sa’adatu, da fatan kin tashi lafiya” Amsa mata nayi da “lafiya lau” Sake mayar da kallonta tayi gare ni. “Yanxun nan Babanki ya kira Abban su ihsan, yace xai zo yanxu sai kiyi sauri ki shirya kada yazo ya jira ki” A xabure na dubeta. “Me kuma zai zo yace Adda?? Har ga Allah ban san zuwan Baba gidan nan, kin san dai ba….” Dakatar da ni tayi “Ki kwantar da hankalinki kuma ki kyautata xato, babu abinda xai faru insha Allah” Haɗa kai nayi da gwiwa ina tunani, Allah yasa dai ba xuwa xai yi ya rusa maganar aurena da izuddeen ba. Komawa nayi na kwan…