TSANANI CHAPTER 15 TSANANI CHAPTER 15 Mijin Adda na shigowa aka nuna masa kayan da doctor ya bani, cikin farin ciki ya hau d’aga kayan ya fara gode masa da wannan ƙoƙarin da yayi min, kallona yayi ya miko min kuɗaɗen da ya bani. “Karbi Sa’adatu kiyi abinda kike ganin ya dace da su” cikin girmamawa na dube shi. “Ku bar shi Abba na bar muku duniya da lahira” Yaji dadin abinda nayi masa sai ya karbi kuɗin yace Adda taje ta kaiwa Innah su yi shawarar a kan abinda ya kamata a siya min da su wanda xai amfane ne ko zuwa gaba. Washe gari bayan nayi shirin makarantar islamiyya, misalin ƙarfe biyu na rana naji kiran wayar doctor cike da nutsuwa nasa hannu na ɗauka tare da kara wayar a kunnena, ban ce komai ba sai da ya fara magana. cikin siririyar muryar shi yace “Salamu alaikum amaryar doctor” ya faɗa tare da rausayar da kanshi Amsa masa nayi da “wa alaikumussalam” ina ɗan sakin murmushin farin cikin sake haduwa da doctorna. Wani ɗan murmushi ya saki, har cikin xuciyar shi yana jin daɗin muryar Sa’adatu, yana mantawa da …