TSANANI CHAPTER 13 TSANANI CHAPTER 13 Karaf naji a kunnena Innah na bawa Adda labarin zuwan doctor wajenta wai yana neman aurena, ba ƙaramin dukan zuciyata maganar tayi ba, zuciyata ce ta fara tafasa naji kamar na fashe da kuka, mamaki ne ya kamani ko ya aka yi ma ya gano gidanmu har ya samu ganin Innah, tambayar kaina na shiga yi, anya Baba ya san abinda ya kawo doctor gidanmu kuwa? Na san ko ya faɗa masa ma baxai amince da aurenmu ba, tunda abubuwa marasa dad’i sun faru tsakaninsu. tsayar da abinda nake nayi na cigaba da sauraren abinda suke fada, shawarar Adda saratu ta nema a kan ta bashi izni yaxo wajena ko kuma a dakatar da shi zuwa wani lokaci? Wani radadi da zafi zuciyata ta hau yi min, a gaskiya yanxu babu niyya ko shirin aure a tare da ni, hasalima ni tsoron maxan nake ji gani nake yi kamar irin halinsu daya da malam Jibo, yaushe har na fito daga tarkon malam jibo da har za a sake kokarin tura ni a wani, a yanxu dai bana burin auren kowane namiji idan ba izuddeen ba, na san shi kaɗai xai iya ri…