TSANANI CHAPTER 13 TSANANI CHAPTER 13 ‘Daya daga cikin kujerun da na ajiye masa ya samu ya xauna yana fuskanta ta, tsananin kunyarsa da kwarjinin sa ne suka kamani, cikin kasalalliyar murya nace “mu’allim barka da dare” kafin ya amsa sai da ya bi ni da wani mayataccen kallo wanda yasa nayi saurin sunkuyar da kaina sannan ya daga baki yace “lafiya lau Sa’adatu” tun daga wannan maganar da nayi ban ƙara cewa komai ba, gyaran murya yayi min har yanzu idanunsa na kaina ya kasa ɗauke idonsa daga kallona, jikina har rawa yake yi ni ban saba da irin wannan kallon ba. + A hankali ya daga bakinsa yace “Na san dole za kiyi mamakin ganina a wajenki kuma a dai-dai wannan lokacin, sbd baki taɓa tsammanin hakan daga gare ni ba” kaina a sunkuye na amsa masa da “eh” Gyara xama yayi cikin siririyar muryar shi ya cigaba da cewa “Tun bayan lokacin da kika bani labarin irin halin da kika tsinci kanki na kasa samun nutsuwa, hankalina ya tashi naji idan har ban kasance cikin rayuwarki na tallafa miki ba nima baxan iya cigaba da …