TSANANI CHAPTER 12 TSANANI CHAPTER 12 Sake bushewa yayi da wata irin dariya wadda har sai da ya tuntsura, Allah ne kaɗai ya san irin muguntar da yake shirin kullawa Sa’adatu wani abu zuciyarsa ke hasaso masa matuƙar ya samu Sa’adatu a yanxu shi kaɗai ya san irin garar da xai kwasa, domin ya dade da sanin Sa’adatu tana dauke da baiwa mai yawa, ƙoƙari ɗaya zai yi shi ne yayi duk mai yiwuwa ta dawo cikin rayuwarsa, tunanin irin lugwigwitar da zai yi mata yake yi, saboda ya san dole yanzu yarintar ta taqara fitowa tunda ta samu huta tare da nutsuwa. + Kamar wanda aka zabura ya tashi ya janyo wata adaka da ke ajiye a gefensa, ya fara fito da wasu irin takardu yana ware wanda zai yi amfani da su fuskarsa na ɗauke da murmushin mugunta. Bincike yake yi sosai sai dai har yanxu ya kasa gano wacce xai yi amfani da ita, wacce da ya xuba aiki xai kama Sa’adatu. Rigingine ya kwanta yana cigaba da dogon tunanin da ya saba. ★★★★★ Salamu alaikum nace sannan na sanya kaina cikin gida. Da murna “Adda saratu ta karɓe nii Sa’a…