TSANANI CHAPTER 11

TSANANI CHAPTER 11
TSANANI CHAPTER 11 Bayan wajen yayi shiru ana jiran umarnin police ya bada damar tafiya ko tsayawa, mikewa Adda saratu tayi tare da cewa ina da magana, damar yin magana ya bata. Gyara tsayuwa tayi tana mai fuskantar mutanen da ke wajen. “Ina ganin yallabai kamar mun yi suya mun manta da albasa, domin kuwa akwai wani abu guda daya da muka manta ba mu yi magana a kansa ba wanda barin nasa ba karamin illa bane ga rayuwar waɗannan bayin Allah, yallabai ina so a shiga tsananin yayata da wannan matar” nuna innah salamatu tayi tare da kafeta da ido, dafa kirji Innah Salamatu tayi, xata yi magana kenan Adda saratu ta katseta ta cigaba da bayani. “Da kuma mijinta sannan da ragowar ƴaƴansu, abinda nake so shi ne yallabai ka jawo hankalin mijinta ya dinga sauke hakkin da ya rataya a wuyansa, sannan ya saurara da cikin zarfinta, ya kamata kuma ya kafawa matarsa da ya’yansa dokoki domin suna take hakkin wadannan bayin Allah ba tare da sun yi musu komai ba, kullum burinsu su zage su sannan su ci musu z…