SAWUN BARAWO CHAPTER5

SAWUN BARAWO CHAPTER5
SAWUN BARAWO CHAPTER 5 WAIWAYE… Asalin su yan garin dutsinma neh dake jahar katsina, amma tun kakanni yawancin su yanayin aiki da kasuwanci ya maidosu garin na gwamna(kaduna) da zama, wanda inhar ba kasanu ba zakai tunanin su d’in yan asalin garin neh. 1 Malam ishak mainasara da rukayya mainasara, sune mahaifa kuma iyaye a gurin Ibrahim,nasiru,da sa’adatu. Ibrahim mainasara wanda yakasance shine uba kuma mahaifi a gurin rukayya(adda) ,Aysha, kabir, safwan, sa’id, salim,ibrahim(khalil), sai auta nabilah. Yayin da nasiru yake da ‘yaya biyu kacal a duniya, Sulaiman da fa’ iza. Autar su kuma sa’adatu dama yaya biyar Allah yabata, Fatima, rabiatu, nasiba, fiddausi sai auta salma. Dukkan su, suna zaune neh a garin kaduna, kuma Alhamdulillah gaba d’aya zuriar malam ishak mainasara Allah ya azurtasu, mussamman alh ibrahim da shi din wani jikakken business tycon neh yayin rayuwar shi, ba shakka yakasance mutum mai matuk’ar kishi da son yanuwan shi Allah yayi mashi rasuwa bayan haihuwar nabila da sheka…