SAWUN BARAWO CHAPTER 9 SAWUN BARAWO CHAPTER 9 Ikon Allah sai kallo! ” cewar innah. + Kana ta rik’e hab’a a yayin da suke bin safwan dake kwance kashirb’an bisa gado da kallo, wanda duba daya zaka mashi ka fahimci dimbin damuwa da tashin hankalin da sukai wa ilahirin rayuwar sa qawanya, mussamamn idan ka diba fuskar shi, babu abin da ya sauya na daga yanayin da ya fada a iya kwanakin da ya dauka a hukumar ta yan sanda. Fuskar nan cunkushe take da damuwa, wanda hakan ya janyo ko burbushin murmushi da fara’ah babu a fuskar tashi, hakan ya faru ne tun bayan artabun da suka buga shi da kabeer din, a inda kabeer din yayi nasarar tserewa ta hanyar rirrike safwan din da akayi ganin yana shirin aika dan uwan nashi barzahu. Yau kusan kwana biyar kenan da afkuwar lamarin, wand daga ranar da Kabeer din ya samu ya kufce bai kuma gigin kallo gidan nasu ba, dukkuwa da irin kiran d hajiyar tasu ta rika mashi akan yazo ayi maganar fahimta, amma gogan naku yai biris yace baesan zance ba, domin kuwa ya riga d ya rantse da mahal…