SAWUN BARAWO CHAPTER 6

SAWUN BARAWO CHAPTER 6
SAWUN BARAWO  CHAPTER 6 Cikin awannin da basu shige biyu ba yagama clearing komi na hotel din, kana suka rankaya gidan dayazama mallakar shi neh cikin gadon shi da mahaifin su yabari. Gida neh madaidaici mai matuk’ar tsari, wanda yake kunshe da madaidaitan falo guda biyu, sai dakunan bacci guda uku kowanne dauke da toilets, sai kuma dangin su kitchen, store, dining area da kuma dakin bak’i. Yanayin tsaruwar gidan neh kad’ai abinda ya birge ramlan har taji tana dan bukatar sanya hakarkarin ta bisa shiryayyen dakin baccin data ke tunanin nan neh nata, ganin yanda tun shigowar su gidan, safwan din ya shiga dayan dakin na can dake k’arshe. Dayake dama anriga da an shirya komi a cikin gidan, hakan yasa bata wani samu matsala ba wajen shiga toilet domin ta watsa ruwa, dama tunda maigadi ya shigo masu da akwatinan su falo ta janyo nata ta shigo dashi dakin. Bayan gama wankan nata neh, ta had’a da d’aura alwalar sallar azahar, duk kuwa da cewa kusan la’asar ma na gaf da yi, amma rashin zama baisa t…