SAWUN BARAWO CHAPTER 4 SAWUN BARAWO CHAPTER 4 Bata jirayi yak’ara wata kalma ba, ta nufi hanyar ko’fa jiki a sanyaye, haka kuma wani sashe na zuciyar ta na ingizata ga wani abin daban. + Bata Kara’sa ficewa ba daga dakin ta tsinci muryar shi yana cewa “Keh kazar mayu make sure you jam the door.” Ilai kuwa tana Kara’sa ficewan ta janyo qofan tai musu jamming, take kuma a gurin ta rasa tudun dafawa, domin kuwa sam bata san inda zata dosa ba a cikin wannan daren, dad’in dad’awa a guri irin wannan da ba ruwan kowa da kowa, in short kowa na mahallin shi a gark’ame. Da yake akwai d’an tazara tsakanin wannan d’aki zuwa wani d’akin, hakan ya sanya tasami wqni d’an passage da taga wata er resting chair a gurin, hakan yasa ta nemi guri ta zauna, diba da yanayi na sanyi da garin ke ciki ya taimaka wajen assasa jin sanyin ta. Hakan ya sanya ta dage k’afafun ta sama, gami da had’e su guri guda ta takure, alokaci guda kuma tana k’ara jan k’aton farin mayafin kanta, domin ya rage mata jin sanyin. 1 Hawaye yacigaba da sauka daga…