SAWUN BARAWO CHAPTER 3

SAWUN BARAWO CHAPTER 3
SAWUN BARAWO CHAPTER 3 A yau ashirin da biyu ga watan satumba, shekara ta dubu biyu da sha shidda, jama’a suka shaida d’aurin auren SAFWAN IBRAHIM MAINASARA tare da Amaryar shi RAMLATU HASHIM TAFIDA, bisa sadaki naira dubu hamsin, lakadan ba ajalan ba. D’aurin auren ya wanzu ne bayan sakkowar masallacin juma’ah na almannar da ke nan unguwar sarki kaduna, duk da d’aurin auren yazo neh b’akatantan ba bisa shiri ba, hakan bai hana jama’ah halartuwa gurin d’aurin auren ba, diba da irin ranar da d’aurin auren ya kasance. Bayan gama d’aurin auren neh, su kabir da sauran k’alilan dangi mafi kusa da suka sami halartar d’aurin auren neh suka rankayo gaba d’ayan su, suka yoh gida, fuskokin su cike da boyayyun al’amura masu wuyar fahimta. Hak’ik’a kusan gaba d’aya mazan gidan basa amanna da wannan auren, amma ganin yanda hajiyar ta su tai tsaye bisa lamarin ya sanya su basar da lamarin ta hanyar bin auren da du’ah’i da kuma fatan dacewa a cikin lamarin. “Lallai hajiya da gaske take fa” cewar sa’id w…