WANI AURE CHAPTER 22 WANI AURE CHAPTER 22 Mikewa Tayi ‘cikin sanyi jiki taje tayo alwala tasoma gabatar da sallar magriba , baita ta Mike daga kan praymat dinta ba har sai da Tayi sallar isha’i. + Kwance take lamo akan gadonta ita daya Tayi shr hannuta rike da karamin litattafin garkuwar muslinci, hisnul muslim. ‘tana dubawa ahankali Amadadin abin da take karantawa ya dinga shiga kwalkwaluwarta sai ma wani tunani ne yazo mata . Sosai ta afka ‘cikin damuwa yayinda tunanin duniya ya taru yayi mata yawa . Tunanin gida da mamanta da mahaifinta har ma da ah’linta, duk shi yafi damun xuciyarta ,ko a wani yanayi en gidansu suke cigaba da rayuwarsu ? Ko wani hali mahaifinta yashiga lokacin daya dawo gida ya iske bata nan ? Allah shine masani …ta fadi hakan ‘cikin zuciyarta ‘tana may langwabar da kanta gefe . ” take nadamar rashin bin umarnin mahaifnta yashigeta, gashi takawo kanta cikin tsaka may inda ba,asan darajarta da mutuncinta ba” to meyye amfanin zuwanta neman kudin shiga Jami,a alhalin mahaifinta…