WANI AURE CHAPTER 19 WANI AURE. CHAPTER 19 Rungume take a faffadan kirjinsa har lokacin ” yayinda hawayen tausayin kanta ke cigaba da bin kuncinta” danasani tattare da nadamar abinda ta aikatawa kanta a can baya ne ke damun zuciya . ‘hakika rayuwa bata da tabbas gashi komai yana neman tsaya mata ” zuciyarta kemata wani irin zafi yau tazo mata tazo mata abu mafi muni ,kishiya …fa. yau ita zeenat da kanta ake kokarin son sanya mijin yi karo mata kishiya… Kishirya.. ta sake maimaita hakan akasan ranta abinda tafi mugun tsana a rayuwarta kennan ,wai aba kishiya .. + kirjinta ke mata radadi da nauyi tamkar an dora mata dutse ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta da gangar jikinta… wani irin maseefaffen kishin mijinta ne ke sake tasomata fiyye da yadda take ji a da. tsanar sauran matan dake duniya zaune bbu aure ne ya dirar mata lokacin. Kukanta yasoma damun tunani ,kasancewarsa mutun marason damuwa da yawan hayaniya. hakan yasa yasoma sausauta rungumar da yayi mata daga qarshe ya ma ra…