WANI AURE CHAPTER 18 WANI AURE CHAPTER 18 Cikin wani irin yanayi wanda kwata kwata ummi bata taba ganinsa ciki ba ya mike tsaye tamkar may koyan magana ya bude bakinsa yanawa ummi sallama. “firt lov ni zan wuce gida yasoma taku cikin isa da kasaita don barin dakin. ,cikin sanyi murya ummi takira sunanshi DEENI… Dan tsayawa yayi Tare da juyowa suna fuskarta juna da ummi idanunta ta xuba mishi kawai Tana kallonsa tare nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sake sauyawa cikin Dan kankanin lokaci. Yasa tace Ka tsaya kaci abinci Dan da alamun kana tattare da wunya,inyaso zuwa anjima Sai ka wuce gida ko..shr kawai yayi yana kallon umminsa. hakika umminsa tafi kowa sanin koshi waye Ta fannin halayyarsa da abinda ke tattare dashi. Sai dai ,shi sam baiji zai iya sawa cikinsa komai a halin dayake ciki damuwarsa dayake tattare dashi , kadai ya ishe sa” ba Sai yaci wani abu , yafison yaje gida kawai domin yana bukatar sake nazari akan maganarsa da ummi. Dan haka ya Dan narkar da fuskarsa alamun baya da bukatar cin wani abu . “…